wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya

wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya

Abubuwan al’ajabi daban daban na faruwa a rayuwa! Rayuwa na ruskar mutane ta hanya daban daban. Idan ka taba jin irin wannan zancen, zaka gane abunda rayuwa ta kunsa.

Kuma ya zama dole mu yarda da cewan rayuwar wasu mutane ya canza saboda basu san cewa zasu zo su samu wani muhimmin abu a rayuwa ba. Suna tafiyar da rayuwarsu a sawwake kuma basu sa a rai cewa wani babban abu zai zo ya canza matsayinsu ba har abada har ma ya zama ana bibiyar su.

A halin ciki, yawancin mata sun san cewa suna sauraron haihuwar da wannan zai sa kaga sun fara shirye-shirye kafin ranar haihuwa. Zakaga suna siye-siyen kaya da zai dace da yanayin lokacin da za’a haifi yaron a ciki.

Babu shakka mace na iya kasancewa cikin mamaki bayan ta haihu barin ma idan dan da ta Haifa ya sha bambam da abunda likitoci suka fada mata a lokacin awon ciki. Mutun zai kasance cikin farin ciki idan ya haifi da mai cikakken lafiya.

KU KARANTA KUMA: An tura Fasto da kaninsa gidan kurkuku na wata shidda

Ga mutanen da suke kokwanton cewa bazai taba yihuwa ace mace tana da ciki amma bata san abunda zata Haifa ba, labarin Taslima Khatun Uno zai canza masu wannan tunani nasu. Ta kasance uwar tagwaye da suka zo a hade, wacce bata san cewa cikin tagwaye take dauke da shi ba saboda likita ya fada mata cewa cikin da daya take dauke da shi.

Uno ta haifi yaranta ta hanyar aiki da akayi mata a wani asibiti dake arewacin Bangledesh kimanin watanni uku da suka wuce. Ita da mijinta basu san cewa yaran a hade suke ba har sai bayan haihuwarsu.

KU KARANTA KUMA: Matukin jirgin shugaba buhari, kyaftin Chinyelu

wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
Rabia da Rukia, kansu a hade
wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
tagwaye
wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
Lokacin cin abinci
wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
Uno tare da yaranta
wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
Wannan abun tausayi ne
wata mata ta haifi tagwaye masu kai daya a maimakon da daya
Uno da Iyalanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng