Hadiza Gabon da Adam Zango sun zama jakadu
- Likkafar Hadiza Gabon da Adam A. Zango ta yi gaba
- Kamfanin taliyar 'yan yara ya nadasu jakadu
- Jaruman za su rika fitowa a duk tallace-tallacen kamfanin
Kamfanin taliyar ‘yan yara ta nada Hadiza Gabon da Adam A zango a matsayin jakadun samfurin taliyarta ta Indomie.
A cewar shafin kannywood.com na yanar gizo, wanda ya bayar da labarin, tare da sa hotunan jaruman biyu suna sa hannu a yarjejeniyar aiki ya ce, Hadiza da Adam sun samu sahalewar kamfanin taliyar ne na zama jakadunsa a tsawon shekara guda.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari yayi kira ga Nollywood
An dai yi bikin sa hannu a yajejeniyar aiki a tsakanin jaruman, da kuma kamfanin taliyar ne, wani gari da ba’a bayyana ba, a kuma hotunan da shafin ya yada, wasu manyan jami’an kamfanin taliyar ne su biyu, suka sa hannu a yarjejeniyar a madadin kamfanin, Hadiza da Adam kuwa, kowa ya sa hannu da kansa.
Wannan jakadancin na nufin fitowa a tallace-tallacen kamfanin a kafofin yada labarai na rediyo, da gidajen Talbijin, da kuma manya-manyan allunan talla, baya ga wasu jerin abubuwa da kamfanin zai yi amfani da fuskokinsu a jiki don kiran kasuwa.
A baya dai, marigayiya Hafsatu Sharada wacce ake kira mai Aya, ta taba yiwa Kamfanin taliyar Jakadiya, a inda ta fito a tallacen-tallacen taliyarsa tare da ‘yan yara, wadanda aka rika sa wa a manya-manyan allunan talla da kuma gidajen Talbijin.
Fitowa a tallace-tallace na daya daga cikin manyan hanyoyin da jarumai a masana’antar shirya fina-finai ke samun babban tagomashi.
Asali: Legit.ng