Gwamnan jihar barno ya nuna tausayi ga jama'arsa
Gwamnan jihar Barno, Kashim Shettima ya bayyana yadda yake yawo a jihar sa ba tare da mota mara jin harsashi ba kwanaki bayan bikin sallan layya.
Jaridar Leadership ta lakwato maganan Shettima inda yake fadama News Agency of Nigeria (NAN) a wata hira da ya gabatar cewa ya yanke shawaran yin hakan ne saboda tausayin jama'arsa da basu da mai kare su sai Allah.
Yanzu kawai ana amfani da motocin ne wajen daukan baki da suke tsoron hari idan suka shiga motoci mara tsaro.
“Muna hannunka mai sanda ga yan ta'addan, inada motoci maras jin harsasshi, amma bani amfani da su. Ina son in kasance cikin halin dar din da sauran jama'a ke ciki.”
KU KARANTA: Abin da ya sa muke rike da Zakzaky- Gwamnatin Tarayya
“Muna da motocin da dama, amma baki kawai muke dauka da su.
“Wani zubin ina tuki cikin gari da kaina domin ganin ma ido na abubuwa.
“Babu wani siddabaru da muke yu , sai da kawai akwai niyyar yi. Babu wani siyasa da yafi gamsar da mutane.
Ba wai kana wurin bane don kai ne mafificin mutum a jihar ba. Ni gwamna je saboda fice da nayi a siyasa, ilimi na, asali da kuma karfi.
“Dalilin wannan shine a cikin ma'aikata na , akwai Wadanda suka fi ni wadannan baiwa. A ra'ayi na mulki abun da ka iya bauwa mutanen ka ne na dan lokacin da kake da shi a matsayin shugaban su.”
Asali: Legit.ng