Kalli abinda coci ke yi da sunan yawon wa'azi
- Mambobin coci n Lord’s Chosen Charismatic Revival Ministries sun dauko wata sabuwar usulubi wajen yin wa'azi a tunaninsu ga jama'a
A wata fita da sukayi, an ga mambobin a wata unguwa suna ta kundunbala a kan titi da sunan yawon daawa
Wannan ya jawo hankalin mutane da dama kuma ana tambayoyi wai shin me ma'anar wannan hauka da suke a kan titi.
KU KARANTA:Wani faston cocin Christ Embassy ya hallaka kansa
Ga hotunan abinda suka dinga yi:
Zaku tuna cewa misalin makonni 3 da suka gabata, da kuma farkon shekaran nan, cocin ta fuskanci sukar bakin jama'a inda aka ga mambobin cocin iyo a cikin ruwan kazanta da sunan wai 'yabon Ubangiji'
Mutanen da dama sun siffanta wannan kundumbalan da suke a matsayin hauka ,kuma shin wannan na cikin aikin wa'azi.
Asali: Legit.ng