Buhari ya tafi kasar Amurka
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga kasar Najeriya domin ya halarci taron United Nations (UN) a kasar Amurka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kuma halarci wani gamuwa tare da shugaban kasar Amurka, Barack Obama a ranara Talata, 20 ga watan Satumba, inda shugabanni guda biyun zasu tattauna kan al’amarin “goyon bayan da kasar Amurka zata ci gaba da bayarwa kan tsaro da canjin tattalin arziki a kasar, haka kuma da kokarin da gwamnati keyi kan kungiyar yan ta’addan Boko Haram.
Shugaban kasa Buhari zai kaddamar da jawabin kasar Najeriya a yayin bude muhawara na taron gaba daya kan “hanya samun ci gaban manufofi: Yunkurin duniya don canza duniyarmu.”
KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC na tuhamar Patience Jonathan
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana musabaha tare da jami'in sa kafin ya ta tashi daga kasar zuwa kasar Amurka. Hoto: Majalisar tarayya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayinda ya yake taka matartakalar shiga jirgin sama da zai kai shi kasar Amurka. Hoto: Majalisar tarayya.
Sai mun hadu bayan na dawo daga ziyarar......Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ban kwana da yan uwa da abokan arziki kafin ya bar babban birnin tarayyar Najeriya.
Hoto: Majalisar Tarayya.
Asali: Legit.ng