Yadda PDP ta jaza tabarbarewar tattalin arziki - APC
Daga Edita: Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) na fuskantar suka daga 'yan Najeriya dalilin tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta shiga. Amma jam'iyyar na dora laifin kan gwamnatin data shude dalilin cin rashawa da almubazzaranci. Ta lissafta abubuwa 27 da suka jefa kasar cikin halin da take.
1. An biya Tompolo N13 biliyan
2. Tsohon shugaban dakarun tsaro, Alex Badeh ya boye $32 miliyan a cikin sokaway
3. Patience Jonathan na ikrarin $31m nata ne, kuma tayi karar kasar
4. Femi Fani-Kayode ya debi N740 miliyan
5. Dasuki yayi amfani da manyan motoci wajen kwashe $35 biliyan daga CBN
6. Olisa Metuh ya debi N400 miliyan
7. Aziboala, wani dan'uwan GEJ ya debi N6 biliyan
8. Nenadi Usman ta debi N3.5 biliyan
9. Fayose ya debi N3 biliyan
10. Obanikoro ya debi N4 biliyan
11. Olu Falae ya debi N100 miliyan
12. Tony Anenih – 400M naira.
13. Oritsejafor – $35M
14. Tsohon shugaban dakarun sama Amosu – 2Biliyan naira
15. Lucky Igbinedion-16B naira
16. Bode-George da Dabo -100B naira
17. Jolly Nyame-2.4B naira
18. Joshua Dariye-700M naira
19. Nyesom Wike ya sace N4b
20. Diezzani da $20 billion kudin man da suka bace?
21. Dala biliyan 15 na sayen makamai da suka bace
22. 10 biliyan naira da aka canza zuwa daloli aka ba wakilai wajen gangamin PDP na kasa
23. Bafarawa ya debi N3 biliyan domin addu'a
24. N12. 7 biliyan na ma'aikatan NEPA da suka mutu sunyi fika fikai sun bace
25. Dala biliyan 20 sun bace daga asusun NNPC
26. Naira biliyan 3 na toshiyar bakin ma'aikatan INEC lokacin zabe
Duk da wannan sace-sacen, wadansu na koken rashin canji, wasu ma cewa suke bita da kullin siyasa ne.
Asali: Legit.ng