Labari mai ban tausayi na wani mutumin Kano dake zaune a birnin Lagas

Labari mai ban tausayi na wani mutumin Kano dake zaune a birnin Lagas

Allah sarki duniya kowa na da buri a duniya da yake so Allah ya cika masa.

A nan wani matashi ne mai suna Mohammed Ibrahim daga jihar Kano. A lokacin da yake dan yaro burin sa shine ya zamo injiniya, amma hakarsa bata cimma ruwa ba sakamakon rashin mahaifansa da ya yi.

Ba a nan kadai ya tsaya ba mafarkin say a zamo tarihi ne a lokacin da hatsari ya afku da shi wanda ya kai ga har sai da aka yanke masa kafar sa ta dama.

KU KARANTA KUMA: Musa: A yanzu ina cikin farin ciki bayan aurena na biyu

Labari mai ban tausayi na wani mutumin Kano dake zaune a birnin Lagas
Mohammed Ibrahim

A yanzu yana da shekaru 30 a duniya amma yance bai yanke imani daga mafarkin sa na son zama injiniya ba, yance ya san wata rana burin sa zai cika duk da cewan abun da kamar wuya.

Mohammed ya ce: “Sunana Mohammed Ibrahim, na fito daga jihar Kano. A lokacin da naked an yaro, ina mafarkin zama injiniya a rayuwa, amma mafarkina ya zamo labara a lokacin da iyayena suka mutu. Abun ya yi kamari ne lokacin da nayi hatsari shekaru goma da suka wuce, wanda ya kai ga har sai da aka yanke mun kafata na dama. Yanzu ina da shekaru 30 a duniya amma ina nan da burin son zama injiniya. Nayi imani, na yarda sannan kuma ina addu’an cewa wata rana mafarkina zai zamo gaskiya koda dai abubuwa sunyi kamari. Wannan shine labara na!

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng