Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Shekaru bai zamo komai ba ga mata; da zaran sun zama iyaye, ayyukansu ya fara. Wannan rawar gani nasu ba zai kare ba koda yaran sun girma.

Wannan tsohuwar matar da kuke gani shekarunta 101 a duniya amma ta kula da nakasashen danta mai shekaru 63 har karshen rayuwar ta; kowa na sa ran mace mai shekaru wannan zata samu matsala ta tafiya ko kuma na tuna wasu abubuwa. Amma duk da tsufar wannan mata bata manta da sunan danta ba.

Ta dauki kaddaran da Allah ya daura mata; ta kula da danta ta kuma kasance farin cikin sa a iya tsawon rayuwarta.

KU KARANTA KUMA:  An hukunta dan Najeriya da aka kama da hodar iblis

Shakuwa dake tsakanin uwa da danta mai karfi ne; abu ne mai taba zuciya sanin cewa duk da dunbin ayyukan rashin imani dake faruwa a fadin duniyarmu ta yau, mutun yana iya samun soyayya mai karfi irin tasu. Wannan labara na uwa da danta zai tuna maka da muhimmancin uwa; zai fada maka gwagwarmayan da iyaye mata ke sha a fadin duniyan nan.

Ta tsinci danta a wani hali da ya zama dole ta yarda da kaddarar da Allah yayi mata; ta sadaukar da tsawon rayuwarta gurin kula da dan nata. Situ Jaleha Yunus, yar uwar tsohuwar mai shekaru 101 tace yayarta ta samu matsala da numfashinta sai aka kaita gurin dan ta a take. Abdul Rahman na tare da ita a lokacin da ta amsa kiran ubangijinta.

Hotunan Abdul Rahman da yake sallamar karshe da mahaifiyarsa ya yi yawo a kaafofin watsa labarai. Kalli wasu daga cikin hotunan tsohuwar mai shekaru 101 da danta mai shekaru 63 a kasa:

1. Meliah da danta

Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Soyayyar uwa da ban ne.

2. Soyayyar uwa da danta

Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Labarin zai taba zuciyar ka har kaji rayuwa ta fice yadda ka dauke ta.

3. Abun tausayi

Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Allah kadai ya san irin radadin da taji ganin danta a haka a matsayinta na uwa.

4. Abdul Rahman na bankwana da mahaifiyarsa

Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Babu shakka wannan da nata zaiyi jimamin rashin uwa daya tamkar da dubu, wacce ke kula da shi iya tsawon rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel