An kama mai ciki da tayi karyan ciki na tsawon watanni 9

An kama mai ciki da tayi karyan ciki na tsawon watanni 9

An kama wata mata da tayi karyan ciki har na tsawon watanni 9

An kama mai ciki da tayi karyan ciki na tsawon watanni 9
Hoton wata mai ciki

An gano wata matashiya wacce ke cikin ganiyar kuruciyarta da karyan cikin har na tsawon watanni 9, bayan an kaita asibiti cikin gaggawa domin haihuwarta.

A cewar Dr Yusuf Abdulraheem, Shugaban likitoci na asibitin Yusjib Industrial medicare dake Ilorin, jihar Kwara, matashiyar tayi nasara gurin yin cikin karya ta hanyar amfani da kaya.

Da yake Magana ga manema labarai a ranar Talata, 13 ga watan Satumba, Likitan yace an kawo  matashiyar da aka kira da suna Azeezat Abubakar, asibitin da sunan haihuwa kamar yadda take cikin halin nakuda, amma ya fara gasganta zarginsa a lokacin da taki yarda a gwada ta.

KU KARANTA KUMA: An kama Abiodun Isreal da miyagun kwayoyi

Ga abunda yace a kasa:

 “Ta kasance tana amfani da sunan asibitin tana karban kudi a gida, ta na fada ma yan uwanta cewa tana awon ciki a Yusjib. Lokacin da yan uwanta suka kawo ta, Na lura cewa ban taba ganin fuskarta ba, amma domin kore kokwanto, na nemi ta dauko katin asibitin ta wanda ta kasa yin hakan.

Bisa rashin kati, sai na bude mata sabon kati; na nemi tazo a duba ta amma ga mamakinsa ta ki, uwar mijin ta ce ta tursasata a yayinda nake kokarin duba cikinta, na gano cewa kaya ta cusa a ciki."

Likitan ya nuna kulawarsa a kan yadda ta dauki tsawon watanni 9 ba tare da an gano cewa karya takeyi ba, ya kuma shawarci iyaye mata da su dunga sanya idanu a kan yayansu mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel