Boko haram sun aika sako ga Buhari cikin wani sabon bidiyo

Boko haram sun aika sako ga Buhari cikin wani sabon bidiyo

- Kungiyar Boko Haram sun aika sakon gaisuwar sallah ga musulmai a fadin kasar

- Sun ce suna cikin farin ciki da koshin lafiya

- Kungiyar Boko Haram sun ce suna son Buhari ya mutu

Kungiyar Boko Haram sun saki wani sabon bidiyo a wannan bakin babban sallah da kayi, sun kuma yi barazana ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Boko haram sun aika sako ga Buhari cikin wani sabon bidiyo

Sun aika sakon gaisuwan sallah ga dukkan yan uwansu a fadin duniya. sun yi addu'an cewa Allah ya kare shugabanninsu, sojojinsu, da Malamansu da kuma ainahin maza da matansu.

kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa kamar yadda arnaye da shugaban kasar najeriya Muhammadu buhari ke yawon fada cewa suna yakar su, sun ce suna nan cikin koshin lafiya, farin ciki da kuma izza.

Ga sakon da bidiyon ya kunsa:

Dan uwa wannan dai wato sallar idi ne ta wannan shekara ta dubu daya da dari hudu da talatin da bakwai (1437) hijiran manzon Allah daga makka zuwa madina, a nan daular musulinci, karkashin jagorancin  abubakar abu muhammad al-Shakawi.

KU KARANTA KUMA: Patience Jonathan ta roki EFCC da ta saki asusunta

Muna isar da gaisuwan sallah ga dukkan yan uwanmu a fadin duniya daga daular musulunci, da kuma musaman shi shugaban mu Imam Abubakar Shekau. Wanda yake shine shugaban ahlu sunnah lil da’awati  wal jihad. Don haka anan gurin kamar yadda Allah ya hada mu gabaki daya, yadda kuma Allah ya hada mu a karkashin wannan inuwar daular musulinci, muna fatan Allah ya kara hada kawunan mu gabaki daya .

Ya kuma doramu a kan al-kitabu was-Sunnah sosai sosai ya kuma azurtamu da kishin addini ya kuma hada kawunan mu ga baki daya. Allah ya bamu nasara a kan kafirai ga baki daya, Allah ya bamu izza a nan dukkannin duniya, Allah ya karemana shuwagabanninmu da kuma sauran yan uwanmu gabaki daya, da malumanmu da sojojin mu, da kuma maza da matan mu.

KU KARANTA KUMA: Tsoro kamar yadda jihar Kaduna ta samu girgizan kasa

Sannan kuma sako zuwa ga ainahin arna wadanda suke yakarmu musaman shi daggatan Shugaban Najeriya wato muhammadu Buhari. Ya sani cewa muna nan a kan addinin Allah kuma kamar yadda suke fada cewan sun gama damu wallahi muna nan a cikin farin ciki, cikin lafiya da izza.

Buhari arne ne kuma muna jiran ganin bayan sa. Ya kasance shugaban kafirai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel