Wani mumunan hadari ya faru a babban titin Lagos-Ibadan
–Wani hadari da ya faru a babban titin Lagos-Ibadan ya bar mutane 5 a mace
–Hakazalika mutane 15 ne suka samu rauni
–Wata mota Mazda tayi kicibis da Mitsubishi bayan an samu wani matsala
Maza hudu da mace daya na aka bada rahoton cewa sun rasa rayukansu sakamakon wani mumunan hadari da ya faru a babban titin Lagos-Ibadan
Wasu mutane 15 kuma sun ji rauni a hadarin da ya faru a misalin karfe 4 na yamma a Ogunmakin,kusa gidan man Total.
Majiya ta bayyana cewa motocin da suka samu hadari su ne Mazda mai lamba KSF477XK da kuma wata mota Mitsubishi mai lamba MUS639DK. An tattara cewan hadarin ya jawo an tare hanyan wucewan mutane. Sai da jami’an hukumar tabbatar da tsaron hanya na jihar Ogun suka dauke motocin a hanya.
KU KARANTA:Anyi shirin jibge sojoji 10,000 a Neja Delta
Yayinda kwamandan FRSC ,Ayobami Omiyale ya tabbatar da cewa mutane 20 ne abin ya shafa. Ya kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni asibitin Ife-Oluwa da Ibadan Centre Hospital.
Ya bayyana cewan direbobin ne ummul khaba’isin hadarin saboda rashin hakuri. “ Muna baiwa direbobi shawaran cewa su dinga hakuri kuma su daina wuce juna musamman a wurarenda aiki ke gudana.”
Asali: Legit.ng