Mutanen wani kauye dake kasar Rasha
1 - tsawon mintuna
Mutanen wani kauye dake kasar Rasha sun tashi sun ga ruwan koramarsu ya gurbace ya koma jini maimakon ruwa.
Wannan abin al'ajabi ya faru ne a wani gari da ake kira Norilsk a kasar Rasha a wata korama da ake kira Daldikhan.
Mutanen wannan yankin sun shaida cewa, lafiya kalau suka kwana -ma'ana ruwan yana lafiya kalau amma wayewar garin ke da wuya suka tarar da ruwan ya gurbace ya koma na jini maimakon Ruwa.
A duniya a hain yanzu, akwai abun mamaki da abun al'ajabi da suke faruwa kullum. Komai da yake faruwa a Najeriya da kasashen waje, Ubangiji yana da ilmi da su.
Asali: Legit.ng