Sarkin Musulmi ya bayyana suwaye 'yan ta'adda

Sarkin Musulmi ya bayyana suwaye 'yan ta'adda

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyana cewa duk wani Fulani makiyayi da ke yawo da makami, dan ta'adda ne daga makwaftan kasashe wadanda ke tayar da rikici da manoma.

Sarkin Musulmin ya yi wannan ikirarin ne a sakon salla da ya gabatar inda ya nuna cewa baragurbi sun yi yawa a tsakanin Fulani inda ya kalubalanci jami'an tsaro kan su dauki mataki na murkushe 'yan ta'addan wadanda ke shigowa Nijeriya da nufin tayar da fitina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel