Fayose yace kasar Najeriya zata kuma inganta
-Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana fatan sa na cewa kasar Najeriya zata kuma inganta
-Ya bukaci yan Najeriya da suyi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa addu’a su kuma roki ubangiji da ya basu wahayi, hikima da kuma ilimin tafiyar da kasar
-Fayose a cikin sakon san a babban Sallah ya bukaci dukkan mabiya addini da su wanzar da zaman lafiya, juriya, hakuri, da kauna ga junan su kamar yadda koyarwan Islama ta tanadar.
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana fatan san a cewa kasar Najeriya zata kuma inganta yayinda ya bukaci dukkan mabiya addinin zaman lafiya, juriya, hakuri, kauna ga junansu kamar yadda addinin Islama ta koyar.
Fayose a sakon san a taya murna ga Musulmai kan bikin babban sallah ya bukaci yan Najeriya dasu yi addu’a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa su kuma roki Allah da ya basu wahayi, hikima da ilimin da zasu tafiyar da kasar.
KU KARANTA KUMA: Jonathan, Atiku, Kalu sunyi makokin Olorogun Micheal Ibru
“Mun kasance yan uwan juna don haka mu zauna cikin lafiya, mu kasance masu juriya a tsakanin mu, kuma mu kasance masu hakuri a wannan hali na koma bayan tattalin arziki wanda zamu bari nan bada jimawa ba,” cewar sa.
Haka kuma, kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya taya jama’ar Musulmai murna kan bikin Sallar wannan shekarar.
A sakon sag a musulmai, daga hannun mataimakinsa a kafofin watsa labarai, Turaki Hassan, Dogara yayi kira g aka masu imani da su yi amfani da wanna lokaci na layya su roki zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasar.
Asali: Legit.ng