buhari ya aika sakon sallah ga yan Najeriya
-Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon murnan babban sallah ka yan Najeriya
-Shugaban kasa yayi Magana kan hadin kai ya kuma bukaci raya ruhin kasar
-Ya bukaci musulmai da su zauna lafiya tare da yan uwansu Kirista
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika da sako ga Yan Najeriya kamar yadda suke bikin babban Sallah.
A wata sanar wa daga Garba Shehu wanda ya kasance babban mataimaki ga shugaban kasa a harkan labarai, shugaban kasa ya bayyana cewa duk da cewan abubuwa na wuya,gwamnatinsa na kokarin aiki domin magance al’amarin.
Ya bukaci dukkan Musulmai da su zauna lafiya tare da yan uwansu Kirista kuma suci gaba da raya ruhin kasar Najeriya.
Yan Najeriya, kamar yadda kuke bikin sallar Layya, Ina jinjina ma hakurinku duk da halin Koma baya da tattalin arzikin kasar ke ciki.
KU KARANTA KUMA: An kama wata yar damfara an kuma yi mata duka a jihar Benue
Halin koma bayan tattalin arzikin da kasar ke ciki a halin yanzu, ya kasance haka ne sakamakon Koma bayan tattalin arzikin a duniya gaba daya da kuma rashin adana da ba’ayi a baya ba. Bazai taba yihuwa a ware yanzu daga da ba domin kurakuran da akayi a da suna damun tayuwar yau da kullun.
Ina baku tabbacin cewa gwamnatin nan tana aiki a kullun domin kawo karshen wahalar da kasar ke fuskanta. Tan gyaran hanyoyi, ayyuka a fannin gidaje, tallafi ga manoma da masu kananan masa’antu, shirin tallafa wa mata da matasa,da dukkan abubuwan da ya dace domin tallafa wa rayuwan talakawa.
Muna samar da tsaro a yanzu. Muna dakatar da cin hanci da rashawa kuma zamu daidaita tattalin arziki da Ikon Allah.
Haka kuma, shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya, Rev Samson Ayokunle ya roki yan Najeriya da su daina kiyayya su kuma runkumi junansu cikin kauna da zaman lafiya yayinda Musulmai suke bikin babban sallah a ranar Litinin, 12 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng