Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kama dan ta'adda a Bauchi

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kama dan ta'adda a Bauchi

Sojojin Najeriya sun kama dan Boko Haram a Bauchi

Boko Haram: Sojojin Najeriya sun kama dan ta'adda a Bauchi

 

 

 

Sojojin Najeriya sun kama wani dan ta’adda na Kungiyar Boko Haram a Jihar Bauchi, kafin nan Rundunar Sojojin ta bayyana yadda ta samu galaba wajen tarwatsa masu barnata bututan man Kasar a Yankin Neja-Delta. Haka kuma dai Rundunar Sojojin ta kashe masu garkuwa da mutane guda 7 a Jihar ta Bauchi.

Rundunar Bataliyar Sojojin Kasar nan ta harbe wasu masu garkuwa da mutane a Ranar Juma’ar nan da ta wuce. Rundunar Bataliya ta 33 ta samu kashe wadannan mutanen na a wani hari da ta kai Ranar 9 ga wata. Mai magana da bakin Sojojin Kasar, Kanar Sani Usman ya bayyana hakan. Kanar din yace sun sami labarin inda wadannan mutane suke, nan take sun ka kai masu farmaki a dajin Lame, nan kusa da Garin Dutsen Ganye a Jihar Bauchin. Inda suka samu nasara a kan su.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun ceto mata da dama a Maiduguri

A jawabin Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Kasar, Kanar Sani Usman yace sun kashe mutanen bayan ba-ta-kashi da aka yi. An hallaka su, kuma an rusa sansanin na su. Sojojin kuma sun yi samu makamai irin su Bindigar AK-47 da sauran su a sansanin. Haka kuma Rundunar Sojojin ta kama wani dan Kungiyar Boko Haram a Jihar ta Bauchi. Rundunar ’Operation LAFIYA DOLE’ dai ta samu nasarar cafke wani dan ta’addan Kungiyar Boko Haram mai suna Adamu Damuna, wanda yanzu haka yana tsare, ana yi masa tambayoyi.

Shugaban Hafsun Sojojin Kasar Lafatanan-Janar Tukur Buratai ya ba Rundunar Sojojin ‘Operation FOREST KUNAMA’ izinin tarwatsa dajin da ke yankin Bauchi da Kasar Gombe domin kama barayi da ‘yan fashi. Har ma an kafa wata Bataliyar Rundunar Sojoji a Dajin na Lame da kuma Burra, hakan zai sa a ga bayan ta’asar da mutanen ke yi.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel