Bincike: 'Yan Boko Haran sun sace ‘Yan mata 3000 a Maiduguri
– Wata Kungiya ta bayyana cewa ‘Yan Boko Haram sun sace mata da yara kusan 3000 tun da aka fara yakin
– Kungiyar ta kira ‘Yan #BringbackOurGirls da su canza salon su
Wani bincike ya nuna cewa Kungiyar Boko Haram ta sace yan Mata da yara kusan 3000 a Yankin Arewa-maso-Gabashin Kasar nan. Kungiyar NPI masu yunukurin kauda fitina ta bayyana wani bincike da ke nuna cewa Boko Haram sun sace ‘Yan mata har kusan 3000 a Kasar nan tun lokacin da suka fara yaki.
Mallam Sahanu Mohammed Idris, shugaban wannan Kungiya mai zaman kan ta watau NPI ya bayyanawa Kamfanin Jaridar Media Trust Ltd a Garin Abuja cewa Boko Haram sun yi awon gaba da mata fiye da 3000. Sahanu yayi wannnan jawabi ne a Ranar Larabar nan. Shugaban Kungiyar ta NPI yace an sace matan ne daga makarantun Musulunci, na Boko, na koyon larabci da kuma na mata.
KU KARANTA: Gwamnan Borno yayi watsi da Mutanen Chibok
Malam Sahanu ya kuma yi kira ga Kungiyar nan ta ‘Bring Back Our Girls’ (#BBOG) da su canza salon su, Kungiyar dai tana neman Gwamnati ta ceto yaran da aka sace daga Garin Chibok. Mala Sahanu yace Shugaban Hafsun Sojin Kasar nan ya bayyana cewa an ceto mata fiye da 20000 kawo yanzu haka, don haka Gwamnati na iya kokarin an kubuto matan da aka sace. Shugaban Kungiyar ta NPI yace abin ba na hawa titi bane ana zanga-zanga kamar za ayi fito-na-fito da Gwamnati.
Kwanan nai dai kuma Farfesa Wole Soyinka ya gargadi yunkurin hana zanga-zangar ta masu #BringBackOurGirls. Sufetan ‘Yan sanda na Kasar dai Ibrahim Idris, ya gargadi su Oby Ezekwesili-da Jama’ar ta, da su guji wannan taron da suka saba. Sufetan ‘Yan Sandan yace akwai barazana ga wannan zanga-zangar ta su. Ya kuma kira su da su nemi izinin Hukuma kafin su fara.
Asali: Legit.ng