Sojoji sun kai farmaki a kauyuka 3 a Bayelsa

Sojoji sun kai farmaki a kauyuka 3 a Bayelsa

Yakin da sojoji suka kaddamar kan tsagerun yankin Neja Delta ya zafafa a ranar Laraba 7 ga watan satumba bayan wani farmaki da  sojoji suka kai a wasu kauyuka uku na jihar Bayelsa.

Sojoji sun kai farmaki a kauyuka 3 a Bayelsa

Jaridar Sun ta ruwaito kauyukan da sojojin suka kai harin sun hada da Peremabiri, Akamabugo da Tikogbene a karamar hukumar Ijaw ta kudu. Ana tunanin harin da sojoji suka kai, wani bangare ne na aikin yaki da tsagerun Neja Delta ne na musamman da rundunar soja ta kaddamar a yankin.

Sojojin da yawansu ya kai 50 sun kai farmakin ne don neman yayan kungiyar Neja Delta Avengers, amma sai suka buge da dukan wasu matasa biyu fasto Lucky da Bernard Ogunawei. Sai dai shedun gani da ido sunce an sako Bernard daga baya, shiko Fasto Lucky sun tafi da shi.

KU KARANTA:Rundunar Sojojin Najeriya ta ja kunnen tsagerun Neja-Delta

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun ruguza gidaje 43, sa’nnan suka tafi da kwalekwalen zamani guda uku. Bugu da kari sojojin sun ruguza gidan daya daga cikin shugaban tsageru mai suna Kwamared Paul mai lakabi Janar Ogunboss, da gidajen sauran tsageru kamar su Million Gobo, Richard Marcus, Elkenah, Bernard Osunawei da sauransu.

Sai dai wasu jama’a mazauna kauyukan sun yi zargin cewa wasu manyan yayan jam’iyar PDP ne suka gayyato sojojin. Wannan ne ra’ayin Janar Ogunboss, wanda yace binciken da kabilarsu ta gudanar ya nuna cewa wasu shuwagabannin PDP ne suka gayyato sojojin sakamakon goyon bayan jam’iyar APC da yake yi. Sa’annan yayi kira ga ministan tsaro, da shugaban kasa Muhammadu Buhari dasu kaddamar da bincike kan harin.

Sai dai kungiyar tsagerun Neja Delta Avengers ta bayyana cewa ta kashe sojoji 20 a yayin aikin ‘Operation crocodile tears’. Kungiyar ta bayyana haka ne ta hannun mai magana da yawunta janar Mudoch inda ya mika gausuwar ta’aziyyarsa ga shugaba Buhari game da mutuwar sojojinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng