Bayani akan Atiku Abubakar

Bayani akan Atiku Abubakar

Wani Edita ya rubuto wanda ayan kasancewarsa zababen mataimakin shugaban kasa na biyu, Atiku Abubakar babban dan kasuwa ne.

Atiku da hadin guiwar wasu aka kafa Intels kamfanin dake ma kampanonin mai ayyuka cikin gida Najeriya da kuma waje. Kuma shi ke da kampanin sarrafa kayan marmari na Adamawa da kuma jami'ar Amurka a Najeriya, dukkansu a garin Yola

Babalola Victor, wani makarancin Legit.ng ya rubutama tsohon mataimakin shugaban kasar wasika inda yake neman aiki a kampanoninsa.

Zuwa ga Atiku, ina mai farin cikin mika gaisuwata a gareka ya shugaba, ina mai tayaka murnar haifuwar jikanka da akayi bada dadewa ba, ina kuma mai yi maka addu'ar tsawon kwanakin da zaka kara samun abubuwan farin ciki irin wannan.

Bayani akan Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Kafin in cigaba, bari in gabatarda kaina. Sunana Babalola Victor, kuma ni hazikin matashi ne mai aiki tukuru domin cin nasarar abinda nasa gaba. Ina sha'awar ilmi da koyo daga hannun kwararru a sana'arsu kuma mai kokarin tabbatarda kammala ayyukan da aka sashi cikin nasara. Amma abin takaicin shine duk da kurucciya ta har yanzu ina cikin neman aikin yi.

KU KARANTA: Shaharren malamin rubuce-rubuce ya kwan dama

Na kammala karatu daga makarantar koyon ilmin fasahar kiwon lafiya koko College of Health Sciences and Technology a Ijero, ta jihar Ekiti, kuma inada takardar sheda ta babbar diploma koko HND a fasahar tsabtace muhalli inda na maida hankali wajen fasahar tsabtace masana'antu da kawar da shararsu. Ni mamba ne na kungiyoyin masu kula da tsabtace muhalli da kuma kungiyar kula da kiyaye hadurra ta Najeriya, koko Environmental Health Officers Registration Council of Nigeria and the Institute of Safety Professionals of Nigeria (ISPON).

Nayi aiki da karamar hukumar Ikole da kuma ma'aikatar muhalli dukkansu a jihar Ekiti. Na kuma yi balaguro da hukumar kwashe shara ta jihar Ondo, hukumar kiwon lafiya ta tashar juragen ruwa a Ikeja, Lagos da kuma asibitin koyarwa na jami'ar jihar Osun.

Ya mai girma Ina da bukatar aiki a Intels a Port Harcourt inda zan iya nuna maka hazakata in ka bani hali, kuma zan taimaka wajen habaka kampaninka. Ina mai fatan zaka duba ka daukeni aiki, inda zan bada tawa gudummuwar cikin kwanciyah hankali da habaka kamfanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel