Shugaba Buhari tare da tsofaffin shugabannin kasar najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsofaffin Shugabannin kasar Najeriya, wanda ya samu halartan manyan masu fada a ji na kasar.
Shugaban kasa Buhari ya jagoranci taron da akayi tare da yan majalisar kasa a majalisa a ranar Laraba 7 ga wata Satumba na shekara 2016, a babban birnin tarayya Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da tsofaffin shugabannin kasar Najeriya, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar da kuma Tsohon Shugaban kasa Cif Ernest Shonekan.
Wasu daga ciki tsofaffin shugabannin kasar basu samu halartan taron ba, ciki harda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da kuma tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya sha bambam kan lokacin da yunwa zai tsaya
Haka kuma rashin zuwan Janar Yakubu Gowan da Shehu Shagari ya janyo hankalin mutane. Taron ya kuma samu halartan manyan masu Shari’ar tarayya guda biyar, gwamnonin jihohi da wasu mataimakan su.
Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar Wakilai, Rt. Hon, Yakubu Dogara basu halarci taron ba.
Dubi hotunan a kasa:
Asali: Legit.ng