Mutuwa ta raba ma’aurata da sukayi shekaru 77 tare
- Hotunan wasu tsofafin ma’aurata ya zagaya yanar gizo da sauri
- Daya daga cikin jikokinsu ya yada wani hoto na bankwanan karshen su
- Mijin na da shekaru 100 a duniya yayin da matar keda shekaru 96 a duniya, ta kusan mutuwa don haka sai suka rike hannayen juna yayinda ita kuma ta mutu
Daya daga cikin wa’adin auren Kirista, ya bayyana cewa ma’aurata zasu kasance tare a gidan aure har sai mutuwa ta raba su. A zamanin nan, sakin aure yana riga mutuwa don haka yana da kyau idan aka ga ma’aurata sun jure a gidan aurensu na wani lokaci mai tsawo.
KU KARANTA KUMA: An harbe yan fashi biyu har lahira a yayinda suke fashi a jihar Lagas
Wannan ne ya kasance ga tsofafin ma’auratan nan da hotunan su ya zagaye yanar gizo cikin sauri. A nan, an gansu rike da hannayensu a kan gado amma labarin dake karkashin wannan hoto zai s aka zubar da hawaye.
Wata mace mai amfani da shafin yanar gizo ta daura hotonsu da rubutun: “Kakata mai shekaru 96, tare da Kakana mai shekaru 100, yan Sa’o’I kafin mutuwarta a karshen makon nan. Shekaru 77 da aurensu. Na san cewa kakanni na ne. Amma wannan hoton shine mafi tausayi da kyau da na taba gani.
Wannan hoto mai karya zuciya ya taba zukatan mutane da dama a fadin duniya yayinda mutane ke nuna tausayawar su ga rashin da kuma soyayyar dake tsakanin ma’auratan biyu.
Asali: Legit.ng