Wasu shahararrun kalamai da suka yi fice a wancan makon
Shahararrun kalamai da suka yi fice a wancan makon.
Mun kawo maku wasu kalamai da suka yi fice a makon da ya gabata. Ga wasu daga ciki:
Zan tarwatsa Najeriya da… -Inji Nnamdi Kanu
Shugaban Kungiyar IPOB mai neman Kasar Biafra mai ‘yancin kai, yace za ya wargaza Najeriya, amma fa da kalamai na gaskiya ba bakin bindiga ba. Kanu dai yana garkame tun shekarar bara.
Kafin a gama gyara, wasu ‘yan Najeriya sun mutu- Sanata Shehu Sani
‘Yan Najeriya suna cikin wani mawuyacin hali, abin da muke tsoro, watakila kafin canjin da aka yi alkawari ya zo, idan har zai zo, mutanen Kasar da dama sun mutu. Sanatan yace watakila kafin Shugaba Buhari ya gama gyaran da yake yi, shi kadai zai rage…
Ban ce ka da Buhari ya nemi tazarce ba-Inji Cif Obasanjo.
Ni ra’ayi na shine, kowa yana da damar ya tsaya takara a Najeriya, ko Muhammadu Buhari ko ma wanene. Tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo yace shi bai ce ka da Buhari ya tsaya takara 2019 ba.
KU KARANTA: Ban ce ka da Buhari ya nemi tazarce ba-Inji Cif Obasanjo.
Idan Sheriff ya ga dama, ya kwana gidan Obasanjo-Inji Ayo Fayose.
Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose yace ziyarar da Shugaban Jam’iyyar PDP, Ali Sheriff ya kai wa Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo duk shirme ne. Idan Sheriff din ya so ma, ya rika kwana gidan Olusegun Obasanjon.
Na fada wa Sheriff, Allah ya jikan PDP-Inji Obasanjo.
Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya fadawa Shugaban PDP Ali Modu Sheriff, bayan ya kawo masa ziyara cewa ya shirya jana’izar PDP, domin a hannun sa za ta mutu.
Wannan sai ya fi Boko Haram… -Inji Sanata Ali Ndume
Sanatan Kudancin Borno yace idan har ba ayi maganin yaro da ke fama da matsalar yunwa ba a Jihar, to za a gamu da rikicin da ya fi na Boko Haram. Idan har ba mu yi komai ba, to Boko Haram ma kadan muka gani.
Asali: Legit.ng