Ministan Birnin Tarayya Abuja ya hana Fulani Makiyaya Kiwo
Minista ya haramta kiwo a Birnin Tarayya
Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya hana kiwon da Fulani suke yi a Garin Abuja
– Ministan ya umarci Hukumar AEPB da ke kula da Muhalli da ta dauki mataki game da Fulanin
– An ba Rundunar hadin Gwiwar damar cafke duk wanda aka kama yana kiwo a Babban Birnin
Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya haramta kiwo Garin Abuja, babban Birnin Kasar Najeriya.
Kwanan ne kuma dai Jihar Ekiti ta sanya hannu bisa dokar da ta haramtawa Makiyayan Fulani yawon kiwo a cikin Garin. Ministan ya umarci Hukumar ‘Abuja Environmental Protection Board’ Watau AEPB da ke kula da Muhallin Garin da duk sauran wadanda ke da dawainiyar hakan da suyi maganin Makiyayan. Ministan ya soki wannan dabi’ar ta Makiyayan, ya kuma yi kira da Jami’an su dauki mataki. Har wa yau dai Ministan yayi kira da Hukomin da su hana tallace-tallacen da ake yi a saman gada a cikin Garin.
KU KARANTA: Nnamdi Kanu zai tarwatsa Najeriya
DailyPost ta rahoto cewa Ministan ya kuma bada umarnin cewa duk makarantar da ba ta samu nasarar akalla kashi hamsin (50%) ba a Jarrabawar WASSCE da NECO na shekarar 2017 mai zuwa, za a kori Shugaban Makarantar daga aiki. Ministan yace abin kunya ne a ce a Garin Abuja ‘yan makaranta na fadi Jarabawar WAEC da NECo na shiga makarantun gaba-da-sakandare. Malam Musa Bello yace ya gaji da ganin yara suna samun kiredit a takardu uku kacal a wadannan jarrabawowi.
KU KARANTA: Nnamdi Kanu zai tarwatsa Najeriya
A baya-bayan nan dama dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawar Kasar nan, Sanata Ike Ekweremadu, yayi kira ga Jihohi da Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar da za ta hana Makiyaya yawon kiwo, haka kuma a kafa wuraren kiwo na zamani a fadin Kasar.
Asali: Legit.ng