Fasto ya kare a ofishin yan sanda kan taimakawa yan bindiga

Fasto ya kare a ofishin yan sanda kan taimakawa yan bindiga

- Yan sanda sun kama wani Fasto mai suna Peretum tare da wata uwar yara bakwai mai shekaru 47 a jihar Lagas

- An kama Fasto din da uwar yara bakwai don karfafa miyagun aiki

- An ce Uwar da ta bayyana kanta a matsayin Jojo ta kasance tana yi wa wasu yan bindiga abinci a jihar

Fasto ya kare a ofishin yan sanda kan taimakawa yan bindiga

Yan sanda sun kama wani Fasto na cocin Cherubim and Seraphim church of Zion da kuma uwar yara bakwai kan zargin ajiye bindigogi da kuma dafa wa yan bindiga abinci.

An rahoto cewa Fasto din wanda ya bayyana sunan sa a matsayin gwamna Peretun, ya karyata zargin.

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa yan bindigan suna daga cikin yan bindiga biyu da aka kama kwanan nan cikin wadanda suka mamaye al’umman Ewedogbon na yankin Igando dake jihar.

Ya kara da cewa yan bindigan yan bindigan sun kai harin halaka ga mazauna garin.

KU KARANTA KUMA: MD ya mutu sanadiyar bin motar bas da ta gogi motarsa

Yan sanda sunce an kama Fasto Peretum tare da wata uwar yara bakwai, Ebimobe JoJo.

Yan sada sun kara da cewa Jojo ta kasance daya daga cikin masu daga wa yan bindigan unguwar Igando abinci. Peretun ya bayyana cewa shi ya taba sana’ar kamun kifi amma ya bar wannan sana’ar bayan ruhu mai tsarki (Holy Spirit), ya umarce shi da ya shiga gari ya kuma kafa coci a nan.

Wanda ake zargin yace yana shirin shiga mota a tashar Iba, domin tafiya jihar Ondo lokacin da yan sanda suka kama shi.

A bangaren Jojo ta bayyana cewa ta kasance tana siyan mai ne daga hannun yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel