Babu Toure acikin gasar

Babu Toure acikin gasar

Kociyan Manchester City, Pep Guardiola bai sanya sunan dan wasan kulob din ba, Yaya Toure, a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su takawa kulob din leda, a gasar Champions League bana.

Daman dai sau daya ne Toure ya buga wasa a kakar nan a wasan da suka yi Stowa Bukarist wanda aka tashi 5-0.

Tuni ake ganin dangantaka ta yi tsami tsakanin Pep Guardiola da dan wasan dan kasar Ivory Coast, Yaya Toure.

Ana rade-radin Toure zai iya barin kulob din kuma ana cewa yana sansana Inter Milan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel