Yan sandan Najeriya sun sha alwashi
1 - tsawon mintuna
A Najeriya, rundunar 'yan sandan kasar ta kaddamar da yaki da barayin jama'a da suka addabi hanyar Kaduna zuwa Abuja a arewacin kasar.
Yakin wanda aka lakabawa suna ''operation maximum security'' zai karade kusan dukkan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Yan sanda sama da 500 ne a yanzu aka jibge a wannan hanya,musamman ma a garin Katari na karamar hukumar Kachia, garin da a 'yan kwanakin nan ya yi kaurin suna wajen sace-sacen jama'a da fashi da makami.
An dai kaddamar da wannan yaki ne domin hana barayi walwala a hanyar.
Asali: Legit.ng