Dan uwan tsohon gwamna Babangida Aliyu ya rasu

Dan uwan tsohon gwamna Babangida Aliyu ya rasu

– Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, yayi rashin dan uwan sa, Alhaji Usman Aliyu

– Usman ya rasu yanada shekaru 67 a asibiti a Abuja.

– Yana daya daga cikin masu aikin Jarida a Nigerian Television Authority (NTA)

Dan uwan tsohon gwamna Babangida Aliyu ya rasu

Jaridar thisday ta bada rahoton cewa Tsohon gwamnan Jihar Neja, Babangida Aliyu, yayi rashin dan uwan sa, Alhaji Usmam Aliyu

Usman ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja da safen alhamis 1 ga watan satumba bayan yayi karamar jinya.

An yi janaizar sa ne a makabartan musulmai inda manyan mutane suka halarta , daga ciki sune dr. Babangida Aliyu da Sardaunan Minna Alhaji Ibrahim Aliyu. Usman na daya daga cikin masu aikin Jarida a Nigerian Television Authority (NTA) na farko.

Najeriya na jiran Ndigbos – Okorocha

Daga baya ya bar aiki a NTA ya bude sabuwar studiyo na shi a shekarun baya kuma shi ne wanda ya fara hayan aikin bidiyo a Jihar Neja.

Yayi ritaya ya zama babban malamin addini, ya wallafa litattafai da dama kuma yan makarantun sakandare na amfani da shi. Kana Usman babban dan kasuwa ne gida da kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel