Buhari ya kai ziyara jihar Osun
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fara gudanar da ziyarar aiki na kwanan daya a jihar Osun a ranar Alhamis, 1 ga watan Satumba.
Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) ta yada bidiyon isar sa jihar a shafinta na Twitter.
Jirgi mai saukar ungulun Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a makarantar kimiyya na Ataoja, Osogbo, inda Gwamnan jihar, Ogbeni Rauf Aregbesola ya jagoranci sauran manyan gwamnati domin su tarbi shugaban kasar.
KU KARANTA KUMA: An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya
Shugaban kasar Najeriya zai kaddamar da kyautar abincin gwamnatin tarayya ga shirin daluban makarantar Firamare da kuma da kuma kaddamar da makarantar gwamnati na Osogbo. Za’ayi taron ne a harabar makarantar.
Buhari ne shugaban kasa na farko da ya kaddamar da aiki a jihar Osun.
Asali: Legit.ng