An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya
-Mambobin Kungiyar Civil Liberties Organisation (CLO) sun zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanya hannu a cikin hare-haren da Fulani makiyaya suka kai jihar Ekiti
-Kungiyar sun bayyana bacin ransu kan rashin kama su bayan kisan kiyashin da makiyaya sukayi ga yan unguwa 13 a Nimbo a ranar 25 ga watan Afrilu
Haushin cewa gwamnati bata sanya baki gurin maganin rikicin Fulani makiyaya a jihar Ekiti ba, yasa kungiyar Civil Liberties Organization (CLO) sun yanke shawarar cewa sakachin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi yana iya yiwuwa yana da hannu a cikin hare-haren koma killa shi ke daukar nauyin su.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta kara kudin shigar motoci filin jiragen sama(Hoto)
Kungiyar ta jadadda cewa abu irin wannan yana faruwa a wata kasa a nahiyar Afrika, Turai ko wani bangare a duniya, da Buhari ya kasanace cikin mutane na farko da zasu fara sukar kashe- kashen amma yana yi kamar babu abunda ke faruwa a kasar sa.
har ila yau, kungiyar CLO sun nace a kan lura da kamu da kuma hukunta Ibrahim Adamumale, 20, wani Fulani makiyayi da ake zargi, an kama a Affa, karamar hukumar Udi dake jihar Enugu, da laifin samunsa da bindigar AK-47 tare da alburusai 24.
KU KARANTA KUMA: Wani matashi ya tashi bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsa (Hotuna)
Bayan haka, kungiyar sunyi Allah wadai da tserewar wasu yan kungiyar da aka kama kan zargin kisan kiyashi a Nimbo a ranar 25 ga watan Afrilu, inda aka kashe yan garin guda 13 duk da sahihanci a idanun fasaha.
Wandanda aka kama kan zargin harin Nimbo sune: Mohammed Zurai, Ciroma Musa, Sale Adamu, Suleiman Laute da kuma Haruna Laute.
Asali: Legit.ng