Joe Hart ya koma Kungiyar Torino

Joe Hart ya koma Kungiyar Torino

– Kungiyar Torino ta dauki aron Gola Joe Hart na Man City

– Kocin Man City Pep Guardiola, ya maida Golan Kungiyar benci

– Man City ta saye wani Golan Barcelona Claudio wancan makon, alamun cewa Hart ba zai ji kamshin raga ba

Joe Hart ya koma Kungiyar Torino

Golan Kungiyar Manchester City da kuma Kasar Ingila Joe Hart, ya koma Kungiyar Torino ta Seria‘ A Italiya na tsawon shekara daya.

Kungiyar Torino ta Italiya ta dauki aron mai tsaron ragar Man City, Joe Hart har na tsawon shekara guda. An kammala wannan ciniki ne a ranar karshe da za a rufe cinikin ‘yan wasa. Golan Ingilan ya dai bar Kulob din na City ne dalilin tunbuke sa da aka yi daga ragar Man City. Sabon Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya nuna cewa ba zai yi da Golan ba, asali ma wasa daya rak ya buga tun zuwan Kocin.

READ ALSO: Hart Zai Tashi daga CITY

Sabon Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya zabi ya saka Willy Caballero a tsakanin ragar Man City din, sai a wani wasan Kungiyar, karo na biyu da Steaua Bucharest ne a wasan zuwa Gasar Champions League yayi amfani da Golan.

Yanzu dai Joe Hart zai kamawa Kungiyar Torino har na tsawon shekara guda. A makon da ya gabata ne Man City ta saye gola Claudio Bravo daga Barcelona, hakan na nufin Joe Hart ya zama na uku cikin jeringiyar masu kamawa Kungiyar. Don haka, ba girma, ba arziki Kocin ya tattara kayan sa ya bar Kungiyar.

Kawo lokacin, Joe Hart na tare da tawagar Kasa Ingila inda yake shirin fuskantar Kasar Slovakia a wasan zuwa Gasar cin Kofin World Cup na 2018, an ba dan wasan dama ta musamman domin tafiya Kasar Italiya an gwada lafiyar jikin sa, ya kuma kammala komawa sabon kulob din na sa watau Torino.

Asali: Legit.ng

Online view pixel