Man City ta saki aron Bony da Nasri

Man City ta saki aron Bony da Nasri

– Man City ta bada aron ‘dan wasan ta Wilfried Bony zuwa Stoke City

– Stoke City ta biya fam miliyan £2m na dan wasa Bony

– Sevilla ta dauki aron ‘dan wasa Samir Nasri

Man City ta saki aron Bony da Nasri

Kungiyar Man City ta Ingila ta tabbatar da bada aron ‘yan wasan ta Samir Nasri da Wilfred Bony zuwa Kungiyoyin Sevilla da Stoke City na tsawon shekara daya.

‘Yan wasan na Man City sun tashi ne sanadiyyar rashin buga wasan da za su fuskanta karkashin sabon Kocin Kungiyar Pep Guardiola. Wani Darektan wasanni na Kungiyar Sevilla Mista Monchi, ya bayyana cewa sun dade suna yunkurin sayen dan wasa Samir Nasri, sai dai Kungiyar ta Man City tayi kokarin rike dan wasan na ta.

KU KARANTA: Su Sanir Nasri za su tashi daga Man City

Duk da cewa kuwa Samir Nasri zai taka leda wannan shekarar a gidan wasa na Ramon Sanchez Pizjuan na Sevilla, babu yarjejeniyar sayen dan wasan na din-din-din. Da alamu cewa dan wasan zai komo Kungiyar sa ta Man City idan har wa’adin aron ya kare.

Haka kuma Stoke City ta dauki aron dan wasa Wilfred Bony kan kudi kusan fam miliyan £2m. Kocin Kungiyar na Stoke City, Mark Hughes yana cewa: “Dauko aron Bony abu ne mai matukar kyau kwarai da gaske, domin kuwa ya san Ingila ciki da waje. Bony ya ci kwallaye da dama a wasan nan.”

Kocin ya cigaba da zuzuta Sabon dan wasan nasa da cewa, Yana da gudun tsiya, ga kuma karfi. A wajen zura kwallo a raga kuma, ba za a bar sa a baya ba. Abin da Kocin yake fada kenan ta shafin Kunguyar na yanar gizo.

Bony yana da shekaru 27 kuma dan Kasar Ivory Coast ne, ya buga wasanni da dama zuwan sa Kungiyar ta City, bayan an sayo sa daga Kungiyar Swansea kan kudi har fam miliyan £28 a watan Junairun 2015. Sai dai ko so daya Pep Guardiola bai taba saka sa a wasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng