Chelsea na zawarcin tsohon dan wasa

Chelsea na zawarcin tsohon dan wasa

– Chelsea na yunkurin sayo tsohon dan wasan ta David Luiz

– Kungiyar na neman ‘yan wasan baya kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa

– Chelsea tayi kokarin sayen Alessio Romagnoli da Kalidou Koulibaly, sai dai abin bai yiwu ba

Kungiyar Chelsea ta lale kudi har fam miliyan £32 domin sayo tsohon dan wasan ta, David Luiz daga Kungiyar Paris Saint-Germain.

Chelsea na neman sayen tsohon dan wasan bayan ta David Luiz daga Kungiyar PSG. Dan wasa Luiz ba ya samun buga wasa karkashin sabon Kocin Kungiyar, Unai Emery. Rahotani sun nuna cewa dan wasa ba ya jin dadin abin da ke faruwa, don haka yana iya barin Kungiyar.

KU KARANTA: Loic Remy da Kennedy sun bar Chelsea

Chelsea dai ta saidawa Kungiyar PSG dan wasa Luiz kan gagarumin kudi fam miliyan £50 shekaru biyu da suka wuce. A makon da ya gabata dai Kocin Kungiyar PSG din ya cire dan wasan bayan ya jawo finariti a wasan su da Kungiyar Monaco. Kungiyar PSG ta sha kashi hannun Monaco a wasan.

Chelsea dai ta koma kan tsohon dan wasan na ta mai shekaru 29 bayan da aka gagara saida mata dan wasan bayan nan na kasar Senegal, Kalidou Koulibaly. Kungiyar Napoli ta ce ko dai a bada Miliyan £60 ko kuma a hakura da dan wasan.

Haka kuma AC Milan tayi watsi da tayin Chelsea din na dan wasa Alessio Romagnoli, Chelsea ta bada har fam miliyan £34, amma Kungiyar tace yaron ba na kasuwa bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel