Sojoji sun jefa bama bamai kan sabon sansanin Boko Haram (Hotuna)

Sojoji sun jefa bama bamai kan sabon sansanin Boko Haram (Hotuna)

- Jirgi mai saukar ungulu ya kai farmaki kan sabon sansanin Boko Haram a jihar Borno

-Boko Haram ta sake sabon sansani bayan nasarorin da hukumar soja ta samu

Sojoji sun jefa bama bamai kan sabon sansanin Boko Haram (Hotuna)
Sojoji

 

Hukumar sojan sama ta kai hare hare kan sabon sansanin Boko Haram wanda ke tsakanin Malam Fatori da Kangarwa dake arewacin Borno cikin daren  29 ga Agusta, wadannan hare hare sun biyo bayan labaran asiri da aka samu cewa wadanda suka tsira daga harin jirgi mai saukar ungulu mai lamba NAF Mi-17 wanda akayi ranar 20 ga Agusta sun taru a wani sabon wuri mai nisan 4-6 km. Wannan ya fito ne daga jami'in hudda da jama'a na NAF Group Captain Ayodele Famuyiwa wanda Legit.ng ta samo.

KU KARANTA : Jini da jini : Murmushin Kada da hawayen kada

Famuyiwa, yaci gaba da cewa: "Ana sa ran hare haren jiragen sama zasu kara gurgunta 'yan ta'addan abinda zai ba sojojin kasa damar yin aikinsu"'

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel