Barcelona ta sayi dan wasan gaban Spain
– Kungiyar Barcelona ta saye dan wasan Kasar Spain dinnan Paco Alcacer daga Valencia.
– Shi kuma Dan wasa Munir El Haddadi ya koma Valencia.
– Alcacer ne dan wasa na shida da Barcelona ta saya daga Valencia cikin shekaru shida.
Dan wasan gaban Kasar Spain, Paco Alcacer ya koma Kungiyar Barcelona inda Shi kuma Dan wasa Munir El Haddadi na Barcelona ya koma Valencia.
Dan wasan gaban Valencia Paco Alcacer ya koma Kungiyar Barcelona bayan an kammala gwajin lafiyar sa, yayin da shi kuma dan wasan Kungiyar Barcelona Munir El Haddadi ya koma Kungiyar ta Valencia. Rahotanni sun nuna cewa Barcelona ta kashe kudi fam miliyan 30 (Na Euros) wajen sayen dan wasan.
An kammala sayen dan wasa Paco Alacer ne yayin da Kasar sa ta Spain ke shirin buga wasar zuwa cin kofin duniya na shekarar 2018 (Da za ayi a Kasar Russia). Kungiyar ta tabbatar da wannan ciniki ne ta shafin ta na twitter, inda kuma ta bayyana cewa dan wasan ta Munir, zai koma Valencia.
KU KARANTA: ARSENAL ZA TA SAYE ALMIRON
Kungiyar dai ta saye dan wasan ne domin ya maye gurbin wani daga cikin ‘yan wasan gaban ta (Messi, Neymar da Suarez) idan har ya samu rauni ko wata larura. Kungiyar tayi yunkurin sayen dan wasan gaban nan Kevin Gameiro, wanda shi kuma ya zabi Atletico Madrid. Ana ganin dai cewa dan wasa Alacer matashi ne mai shekara 23 a duniya, don haka ba zai damu idan har an ajiye sa a benci ba.
A bara dan wasa Alacer ya ci kwallaye 15 cikin wasanni 40 da ya buga gaba daya, dan wasan dai ya ci kwallaye za su kai 72 a rayuwar sa, tun bayan da ya fara buga manyan wasanni shekaru shida da suka wuce. Barcelona dai ta sayi ‘yan wasan Kungiyar Valencia da dama cikin ‘yan shekarun nan, sun hada har da: Andre Gomes, Jeremy Mathieu, Jordi Alba da kuma David Villa.
Asali: Legit.ng