Arsenal za ta saye wani dan wasan tsakiya

Arsenal za ta saye wani dan wasan tsakiya

 

– Kungiyar Arsenal na gab da sayen wani dan wasan tsakiya mai suna Miguel Almiron.

- Arsenal are closing in on a deal for Miguel Almiron, Paraguayan 22-year-old star

– Dan wasan zai kai akalla fam miliyan €13m

– Almiron zai biyo sawun su Shkodran Mustafi da Lucas Perez.

Arsenal za ta saye wani dan wasan tsakiya

Kungiyar Arsenal na neman wani dan wasan tsakiya, Miguel Almiron dan Kasar Paraguay mai shekaru 22 da haihuwa.

Arsenal na shirin sayen dan wasan tsakiya, Miguel Almiron dan asalin Kasar Paraguay kafin a rufe kasuwa. 90min.com sun rahoto daga Tuttomercatoweb cewa Arsenal din na tattaunawa da Kungiyar dan wasan watau Club Lanús, ana kuma sa ran hakar ta cin ma ruwa kafin Ranar Laraba, da za a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa.

KU KARANTA: ARSENAL ZA TA KARA DA PSG A CHAMPIONS LEAGUE

Majiyoyin sun nuna cewa Arsenal za ta lale kudi har kusan fam miliyan €13m wajen kawo dan wasan Emirates. Dan wasa Almiron mai shekaru 22 a duniya yana bugawa Kungiyar Lanús ne ta Argentina, a baya ya bugawa Kungiyar Cerro Porteño sa’ilin yana matashi, kafin shekarar 2015.

Miguel Almiron ya bugawa Kasar sa ta Paraguay wasa a Gasar Copa America ta aka buga wannan shekarar. Idan dai har wannan ciniki ya yiwu, Arsenal din ta saye ‘yan wasa da kusan uku kenan cikin ‘yan kwanakin nan. A ranar Asabar din ta wucen nan ne Kocin Kungiyar ya bayyana cewa ya sayi dan wasan bayan nan na Kasar Jamus, Shkodran Mustafi daga Valencia da kuma dan wasa Lucas Perez.

Kocin na Arsenal, Arsene Wenger dai ya gamu da suka da dama daga magoya bayan Kungiyar bayan da ya ki sayen wani dan wasa ban da Granit Xhaka. Watakila hakan ta sa yanzu ya dunguma cikin kasuwar hada-hadar ‘yan wasan. Kungiyar dai ta saye ‘yan wasan da suka hada da Kelechi Nwakali, Rob Holding da kuma Takuma Asano, sai dai ta bada aron dan wasa Asano.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel