Hira da Dan auta cikin Kakakin Majalisun Najeriya

Hira da Dan auta cikin Kakakin Majalisun Najeriya

Hira da Dan auta cikin Kakakin Majalisun Najeriya.

Hira da Dan auta cikin Kakakin Majalisun Najeriya

Aliu Sabiu Maduru, mai shekaru 33 a duniya, shine kakakin Majalisar Jihar Katsina, kuma yana cikin ‘yan majalisun Najeriya masu kananan shekaru a Kasar yayi wata tattaunawa, inda yayi magana game da matasa, siyasa da sauran su.

Ko za Ka ba mu takaitaccen tarihin ka?

Sunana Aliyu Sabiu Ibrahim. An haife ni a Kauyen Muduru na Garin Mani, Jihar Katsinaa ranar 5 ga watan Junairun, 1983. Nayi makarantar firamare a Muduru Model Primary School daga shekarar 1988 Zuwa 1994, daga nan kuma na wuce Usman Dangogo College of Arabic and Islamic studies, Wanda aka fi sani da ‘Arabic Teacher’s College’. A nan na koyi larabci da kuma turanci, wani abin sha’awa, na hardace Kur’ani ina aji na 1 na Babbar Sakandare (SSS1). Na kuma wakilci Jihar Katsina da ma Najeriya a Gasar Karatun Al-kurani na Kasa.

Wace makaranta ka tafi bayan ka share wadannan?

Na wuce zuwa ‘Hassan Usman Polytechnic’ inda na samu shaidar Diploma a fannin Sharia daga 2003 zuwa shekarar 2006. Daga nan na samu zuwa Jami’ar Al-Madinah da ke Kasar Malaysia, ma karanci ilmin Komfuta da IT a matakin digiri. Na kuma yi aiki a matsayin mai bada shawara (Watau PA) a ofishin Rajistara na Jami’ar.

Mun samu labarin cewa kamar ka taba koyarwa a Firamare da can ko?

Kwarai, anyi haka! Bayan na kammala karatun Diploma nayi aiki a makarantun Firamare na Jihar na tsawon shekaru uku, daga 2006 har 2009 a Garin mu. Da ma can ina son koyarwa, kai har makarantar Islamiyya na bude a Kauyen mu mai suna Ta’afizul Qur’an L’arabiya tun a shekarar 2002, yanzu haka akwai dalibai sun fi 300.

To me ya kawo ka siyasa?

Bayan na dawo hutu Najeriya, lokacin ina karatun digiri na biyu, dattawa suka same ni, suka ba ni shawarar in shiga wannan harka, da fari nace, Sam! Haka aka tursasa ni, na shiga Jam’iyyar APC, na kuma ci firamare.

KU KARANTA: MATASAN BAUCHI SUN CACCAKI GWAMNAN JIHAR

 

(A KARANTA CIKKAKKIYAR FIRAR A GABA)

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: