Hawa'u Sale na neman taimako cikin gaggawa

Hawa'u Sale na neman taimako cikin gaggawa

-Hauwa’u Sale na neman taimakon gaggawa

-Yar talakawan tana bukatar naira 500,000 ne kawai domin magani

-yar shekaru 13 mazauniyar Kauyen Yan Doma dake jihar Katsina ce

Hawa'u Sale na neman taimako cikin gaggawa
Hawau Sale, mai neman taimako

Hauwa’u Sale yarinya ce mai shekaru 13 a duniya, tana zaune a Kauyen Yan Doma, dake karamar hukumar Ingawa, na jihar Kartsina. Kimanin shekaru biyu kenan da Allah ya jarabce ta da wani babban cuta, wacce ta yadu a saman fuskarta, har ya kai ga ruwa yana tsiyaya a idanunta.

A yanzu haka Hauwa'u na neman taimako cikin gaggawa, kuma Iyayen ta talakawa ne, an kaita asibitin koyarwa na Ahmadu Bello dake Zariya, likitoci su duba cutar dake damun fuskar Hauwa’u, sun kuma nemi su biya kudi naira dubu dari biyar (500,000) domin yi mata aiki. Hakan ne yasa Iyayenta suka fauwala wa ubangiji lamarin domin basu da wadannnan makudan kudin kuma babu inda zasu same su.

Tsawan lokutan da tayi da wannan cutar, sai kara gaba yakeyi in yake ta nakasa Hauwa’u, sun nemi taimako daga jama’a amma shiru kakeji har yau basu sami tallafi ba.

KU KARANTA KUMA: Duba Amare 6 da suka samu mugayen masu kwalliya a ranar aurensu

Ina Kira gareku jama’a masu Lafiya da masu Arziki, bance taimakon Hauwa'u ya zama tilas a gareku ba, kamar yadda nima bai zama tilas akan na turo bukatarta anan don taimaka mata ba.

Amma ku tuna da cewan, zamu haihu wata rana, ko me zai samu dan namu? Akwai fa cutar da kudi ba sa iya maganinta, kowa za yi mana maganinta nan gaba? Ka taimakawa wanda ke neman taimako koda ba ka san shi ba, Allah zai taimaka maka silar wanda baka sanshi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng