Tsohon Dan Wasa Yobo zai bugawa Kano Pillars

Tsohon Dan Wasa Yobo zai bugawa Kano Pillars

– Tsohon dan wasan Super Eagles, Joseph Yobo zai bugawa Kungiyar Kano Pillars.

– Dan bayan na Kungiyar Everton ya ajiye kwallon kafa ne a shekarar 2014.

– Kungiyoyi da dama suna kokarin janyo dan wasan ya buga masu.

Tsohon Dan Wasa Yobo zai bugawa Kano Pillars

Tsohon dan wasa kuma kyaftin na Super Eagles din Najeriya, Joseph Yobo zai bugawa Kungiyar Kano Pillars kwallo.

Kungiyar kwallon kafar nan ta Najeriya Kano Pillars, ta tabbatar da cewa Tsohon kyaftin din Super Eagles na Najeriya Joseph Yobo, zai buga kwallo tare da su wannan shekarar. Dan wasan zai bugawa Kungiyar ta SAI MASU GIDA wannan karo, duk da cewa Gasar shekaran ya kusan zo karshe.

KU KARANTA: KOCIN INGILA ZAI AJIYE RASHOFORD IDAN HAR BA YA BUGA WASA

Joseph Yobo ya fara kwallo ne da Kungiyar Michelin FC ta Garin Fatakwal, Kwanan nan dai aka nada Tsohon dan wasan a matsayin jakada, Hukumar da ke kula da Kungiyoyin kwallon Kafa na Kasar suka ba sa wannan aiki.

Idris Malikawa, wanda shine mai-kula da yawun-bakin Kungiyar Kano Pillars ya bayyanawa Legit.ng cewa Tsohon dan wasan Najeriya, Joseph Yobo zai buga kwallo tare da su. Ko Sani Kaita, wani dan wasan na Najeriya, ya bugawa Kungiyar Ifeanyi Ubah ta Kasar. Malikawa yace:

“Hakika, ina iya tabbatar maka da cewa Yobo Joseph zai buga kwallo da mu, kuma wannan ba karamin abu bane da ma Gasar Premier league ta Najeriya gaba daya, za ya taimaka da kwarewar sa”. Idris Malakiwa ya cigaba da cewa: “Yobo, dan wasa ne da kowa yake son ya zo ya kalla, duk da cewa ya ajiye kwallo a gida, za mu yi kokarin ganin cewa ya samu jin dadin da duka ake bukata a nan, Kano.” Malikawa dai ya tabbatar da cewa lokacin da yake magana, Yobo na tattauna da jami’an Kungiyar ta Kano Pillars, Ya bayyana Yobo na farin ciki da hakan.

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: