An nada tsohon dan wasa Ronaldo aiki a Real Madrid

An nada tsohon dan wasa Ronaldo aiki a Real Madrid

– An nada Tsohon dan wasa Ronaldo, matsayin Jakada kuma mai-bada shawara a Kungiyar Real Madrid.

– Gwarzon dan wasan na Kasar Brazil zai fara aiki nw watan gobe.

– Ronaldo ne ya karbi kyautar dan wasan duniya a shekarar 2002 lokacin yana Real Madrid.

An nada tsohon dan wasa Ronaldo aiki a Real Madrid

An nada Tsohon dan wasan Kasar Brazil dinnan Ronaldo de Lima, a matsayin Jakada kuma mai-bada shawara a Kungiyar Real Madrid.

Tsohon dan wasan kwallon Real Madrid ya dawo Kungiyar, wannan karo ya dawo Bernabeu ne a matsayin Jakada kuma mai-bada shawara game da harkokin kwallon kafa. Tsohon dan wasan mai shekaru 39 zai yi aiki tare da Shugaban Kungiyar Florentino Perez, Perez din ne dai wanda ya sayo dan wasan a shekarar 2002 kan farashi fam miliyan £36.3 daga Kungiyar Inter Milan.

Jaridar Marca ta rubuta cewa, Ronaldo zai fara aikin ne a watan Satumba, inda zai yi aiki tare da Kocin Kugiyar, kuma tsohon abokin aikin sa, Zinedine Zidane. A baya dai, Kungiyar ta nemi dan wasan da ya dawo, sai dai wani aiki ya rike sa a Kasar sa, yayi kokarin ganin an buga Gasar World Cup na 2014; Brazil, ba tare da matsala ba.

KU KARANTA: MOURINHO YA SAKI DAN WASA

Ronaldo ya jefa kwallaye 107 cikin wasanni 117 da Kungiyar ta Real Madrid, Hakan ya sa ya zama cikin manyan ‘yan wasan Kungiyar a Tarihi. Ronaldo ya bugawa Kungiyoyi da dama, irin su; PSV, Barcelona da kuma Inter Milan.

Ronaldo ne ya lashe kyautar dan kwallon duniya har sau uku a rayuwar sa, 1996, 1997 da kuma shekarar 2002, lokacin yana bugawa Real Madrid. Kwanan nan dan wasan ya fitar da manyan yan kwallon sa guda 11, sai dai bai zabi takwaran sa ba na Real Madrid, amma ya sanya Lionel Messi na Barcelona.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: