Takaici! 'Yan Najeriya 241 sun iso daga Libya
-Yan Najeriya 241 sun iso filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos ranar 23 ga Agusta
-'Yan Najeriyan suna komowa ne daga Libya bayan samun matsala da jami'an shige da fice
-NEMA ta karbe su, tayi kuma alkawarin kula da su da kuma tsugunna dasu
Kwatankwacin 'yan Najeriya 241 suka iso filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMA) Lagos ranar Talata 23, ga Agusta. Sun dawo ne sakamakon matsalolin da suke fuskanta da zaman su a kasar Libya. Ana kiran irin wadannan mutane da suka dawo Masu Dawowa da Taimako. Jirgin kasar Libya kirar Airbus A330-200 ya kawo su inda suka cika dakin jiran jirgi da kayansu.
Guardian ta ruwaito cewa mafi yawansu sun makale a Libya dalilin rashin sa'ar ketara tekun Mediterranean zuwa Turai. Wasunsu an jefa su wakafi dalilin matsaloli da jami'an shige da fice, kuma da yawansu 'yan shekara 15 zuwa 25 ne da kuma kananan yara. An kai hudu daga cikinsu asibiti nan take domin suna fama da ciwuwwuka daga harbin bindiga. Hukumar kasa da kasa ta masu tsallake iyaka koko The International Organisation for Migration (IOM) ta shirya maido su gida bayan sun nuna sha'awar dawowa.
KU KARANTA : Sojojin Bangladesh sun jinjinawa na Nigeria
Wannan shine karo na ukku da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) tare da hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) suke daukar dawainiyar kula da masu dawowa. Wani jami'in IOM dake Lagos Nahashon Maina Thuo, yace za'a taimakama kowannensu da N15, 000 domin komawa jihohinsu na asali. Za'a taimakama wasunsu fara kananan sana'u, yayin da za'a taimakama maras lafiya cikinsu wajen biyan kudin jiyya
Daraktan Taimako na hukumar NEMA Aliu Bafada Sambo yace hakkin hukumarsa ne ta amshesu daga IOC, tsugunnad dasu tare da maida su garuruwansu
Asali: Legit.ng