Wata mata yar shekara 65 ta rasu a rijiyan Masallaci.
–Wata mata mai shekaru 65 ,mai share masallaci ya rasu cikin rijiyan masallaci
–Maragayiyar,wacce ta kasance mai yin aikinta na gyara masalacci bata samu wanda zai ceceta ba.
An tsince gawar Wata mata yar shekara 65 mai suna Iya Majeobaje a cikin rijiyan masallaci a garin ilori, babban birnin jihar kwara.
Game da cewar Jaridar Thisday, a bayyana cewa hadarin ya faru ne a masallacin kungiyar Ansaru Deen sa ke Osere, Sawmill a jihar.
Maragayiyar,wacce aka sani da aikin sharan masallaci da gyara shi ta fada rijiyan masallacin ne a ranan juma'a 19 ga watan agusta misalin karfe 5.00 na yamma yayinda ta ke jan ruwa domin gyara masallaci. Abin takaici, babu wanda ke cikin harabar masallacin a lokacin a lokacin da abin ya faru, sai dai aka fiti da gawat da a ranar asabar , 20 ga watan agusta da rana.
Game da cewar wani idon shaida, babu mutane a masallacin a lokacin, amma, wasu mazaunan da suka lura da abin,suka kira ma'aikatan kashe wutan da ke ilori. Diraktan Hukumar kawo agajin kashe wuta na jihar, Tiamiyu raji ya tabbatar da labarin. Raji yace daya daga cikin ma'aikatan su ne ya ciro matan daga cikin rijiyan.
KU KARANTA : Wani mutumi ya lalata yarinya yar shekara 7 a cikin masallaci
Kakakin yan sanda na jihar, Ajayi Okasanmi yace : “Labarin gaskiya ne, matar yar shekara 65 cd. Bamu samu rahoton wani ba dai dai ba ,amma ana gudanar da bincike.”
Asali: Legit.ng