Barcelona da Manchester City sun sanar da sabuwar cinikayya.
- Guardiola yana zawarcin Claudio Bravo.
- Barcelona sun tabbatar da tattaunawa da Barcelona.
- Wata kila Bravo zai tafi City akan yuro miliyan 16.
Robbert Farnendez, wanda shine sakataren zantarwa na kungiyar Barcelona ya tabbatar mana da zantawar da sukayi da Man City. A baya mun bayyana cewar , Guardiola ya yarda da sayan dan wasan dake tsaron ragar kungiyar kwallon Barcelona Claudio Bravo, akan kudi yuro miliyan 16, sai dai kin saka dan wasan su wato Joe Hart a wasan da Man city ta lallasa sunderland. Ana tunanin dan wasan na Ingila zai bar kungiyar.
Wani wanda yake kusa da dan shekara 29 yace, Pep Guodiola dakuma Joe Hart, basa wani jituwa tunda ya amshi aikin kungiyar ta Man City. Fernendez yace “ mun fara Magana kan yarjejeniya tsakanin mu da kungiyar Man city kan dan wasan su maisuna Claudio Bravo. Muna jiran faruwar lamarin nan da sati daya”.
Fernendez ya kara dacewa, “ Idan Bravo ya tafi, muna fatan samun sabon mai tsaron ragarmu”.
Asali: Legit.ng