Allah daya-gari bam-bam! Lefe hadda alade a wata kabila
Sanin kowa ne dai lefe wasu kaya ne da ake kaiwa gidan amarya a duk lokacin da zatayi aure. Ana kai lefe ne daga wurin miji kokuma dangin sa.
Kamar yadda Allah ya banbanta mu a kabilu-kabilu, haka ma kuma kowace kabila tana da irin nata salon na yin lefe dai-dai da al'adunta. A Najeriya wasu kabilu kamar na Kanuri dake a jihar Borno da kuma Ibo dake kudu maso-gabashin Najeriya sukan tsauwala yayin da iyalin mata kan bukaci abubuwa masu tarin yawa daga dangin miji a matsayin lefe wanda kuma wasu kabilun nasu babu tsada sosai.
A wani labari da aka wallaba a shafin sada zumunta na fesbuk na wani lefe da aka kai wa wata mai shirin zama amarya hadda alade a ciki. Kai ala dun ma bama daya ba ba biyu ba.
Sauran kayan lefen da aka kai sun hada da akuya baka, katan din kifi, buhunnan shinkafa da kuma kwalaben giya da dai sauran su.
Asali: Legit.ng