‘Yan wasan da suka samu matsala da Pep Guardiola

‘Yan wasan da suka samu matsala da Pep Guardiola

‘Yan wasan da suka samu matsala da Pep Guardiola.

Ba abin mamaki bane, kuma hakika ba yau Pep Guardiola ya fara samun matsala da manyan ‘yan wasan da yake horarwa ba. Kawo yanzu zuwan sa Man City, ya samu matsala da wasu manyan yan kwallon Kungiyar irin su Joe Hart da Yaya Toure, bisa dukkan alamu kuma, dole su tashi. Kafin nan din Kocin ya samu matsala da wasu ‘yan wasan a Barcelona da Bayern Munich, wanda hakan ta sa dole su ka bar kulob dinnan nasu. Ga wasu daga cikin ‘yan wasan da Guardiola ya tursasa suka tafi suka bas a wuri:

‘Yan wasan da suka samu matsala da Pep Guardiola
Guardiola rift

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DECO:

Guardiola ya samu matsala da Deco a Barcelona, Kocin yana ganin cewa Dan wasan na Kasar Portugal na iya kawo masa tangarda a Kungiyar saboda yanayin dabi’ar sa. Ganin dai ba za ayi da shi ba, Deco ya tattara ya koma Kungiyar Chelsea ta Ingila.

ETO’O

Tun a tashin farko, Guardiola ya bayyana cewa ba abin da zai yi da dan wasa Samuel Eto’o na Kasar Kamaru, hakan kuma ta faru, duk da dan wasan ya ci kwallaye kusan 40 a shekarar, Guardiola ya sallame sa ya kawo Zlatan Ibrahimovic.

RONALDINHO

Dan wasan duniya har sau biyu, Ronaldinho, ya bar Barcelona dalilin Guardiola. Duk da cewa dan wasan na Brazil ya ci wa Kungiyar Kofin UEFA Champions league, amma hakan bai sa Pep ya ajiye sa ba.

KU KARANTA: YAN WASAN DA GUARDIOLA KE SHIRIN KORA DAGA MAN CITY

YAYA TOURE:

A shekarar 2009 Guardiola ya nemo Sergio Busquets, hakan kuma ya say a ajiye Yaya Toure daga wurin sa a tsakiya. Bayan ya ci kofin UEFA Champions League, dan wasan bai yi wata-wata bay a bar Kungiyar.

ZLATAN IBRAHIMOVIC

Bayan ya saida Eto’o, ya kawo dan wasa Zlatan, amma sai da ta kai ba a ga maciji tsakanin dan wasan da Koci Pep Guardiola. Daga baya, dan wasan ya koma AC Milan bayan an kashe makudan kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: