An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)

An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)

Wani mai amfani da shafin sadarwan Facebook, Kadiri Ismaila, ya bada labarin yadda aka kama wata tsohuwa ta sato matacen jariri a yankin Oshodi dake jihar Lagas.

Bayan an kama tsohuwar, an sa ta kewaye gurin dauke da gawan jaririn a bayan takafin a mika ta hannun yan sanda. Karanta yadda ya bayar da labarin lamarin mai rikitarwa a kasa:

“An kama wata tsohuwa a yau da hantsi, tare da gawan jariri mai kimanin wata 1 da haihuwa da ta sato a yankin Oshodi na jihar Lagas. Abun al’ajabi basa karewa.”

An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)
An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)
An kama wata tsohuwa da gawan jariri a jihar Lagas (Hotuna)

Yan sanda sun saki tsohuwar matan da aka kama tare da gawan jariri a jihar Lagas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa masu tafiya a hanya sun kama matar da aka kira da Kuburat Ayinde a hantsin ranar Litinin a Oshodi karkashin gada, sun kuma zarge ta da sace jariri dan wata daya da haihuwa goye a bayan ta. A lokacin da chunkoson mutane suka gano cewa yaron ya mutu, sunyi zanga-zanga a kan matar wadda daga bisani wasu yan sanda a Oshodi suka cece ta.

A lokacin bincike, matar ta bayyana cewa matacen jaririn jikanta ne. ta ci gaba da cewa tana hanya kais hi asibiti ne ya cika, cewa mahaifiyar yaron na da ciwon hauka. An hado cewa yan sanda sun tsare matar domin suyi bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Bisa ga kwamandan yan sanda, Dolapo Badmos, an saki matar bayan mahaifiyar yaron da kuma sauran ahlin gidan sun zo ofishin yan sanda kuma sun bayar da bayani da yayi daidai da na tsohuwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng