‘Yan wasan da Guardiola ke shirin kora daga Kungiyar Man City

‘Yan wasan da Guardiola ke shirin kora daga Kungiyar Man City

‘Yan wasan da Guardiola ke shirin kora daga Kungiyar Man City

Sabon Kocin Kungiyar Man City ya fara da ajiye manyan ‘yan wasa irin su Yaya Toure, Samir Nasri, Wilfried Bony, Eliaquim Mangala, da ma Gola Joe Hart a benci. Legit.ng na lura da irin abin da ke wakana a Kungiyar karkashin sabon mai horaswar, don haka muka kawo maku jerin ‘yan wasan da Kocin zai yi kokarin saidawa.

‘Yan wasan da Guardiola ke shirin kora daga Kungiyar Man City

Yaya Toure:

Da alamu dai Yaya Toure zai bar Kungiyar ta Man City, sai dai kuma wane Kulob ne za su iya biyan sa albashin da yake karba na £220,000 a kowane mako? Dan wasan ba zai ki zama ba har kwantiragin say a kare ko kuma ya samu Kungiyar da za ta iya biyansa wannan makudan kudi.

Samir Nasri:

Guardiola ya ba Dan wasa Nasri umarnin aiki shi kadai domin ya dawo ya samu ya rage kiba, Kocin ya bayyana cewa dan wasan yayi kiba da yawa don haka sai ya rage teba, da alama dai kwanakin tsohon dan wasan na Arsenal sun kare a Manchester.

KU KARANTA: JOE HART ZAI BAR KUNGIYAR MAN CITY

Bony:

Ana ganin cewa dan wasa Bony bai dace da irin kwallon Pep Guardiola ba, Kungiyar ma tayi kokarin yin yajejeniyar kakara da shi wajen sayen Dan wasa Stones daga Everton. Dole dan wasa Wilfried Bony ya bar kungiyar kan kudi kamar fam miliyan £13.

Eliaquim Mangala:

Ba shakka kudin da aka cire har miliyan £45 wajen sayan Mangala yayi yawa. Mangala dan baya ne mai yawan kuskure da shirme, asali ma ko tare bai iya ba a matsayin san a dan baya. Guardiola na kokarin sakin dan wasan, AC Milan da Valencia suna cikin masu zawarcin sa.

Jason Denayer:

Ganin akwai yan baya da dama irin su Mangala, Otamendi, Kompany da ma Stones, Denayer ba zai samu gurbin bugawa ba, don haka dole ya tashi ya bar Kuniyar, tuni ma irin su Swansea sun fara neman matashin.

Joe Hart:

Da alama dai Golan Kungiyar zai tashi, Pep Guardiola ya gwammace ya sa Willy Cabalerro a raga maimakon Golan farko na Kungiyar da ma Kasar Ingila. Guardiola dai yace watakila wasan nan gaba ya fara da Golan. Amma dai ina bukatar mai hanzari, kuma Cabollero ya fi dama a yanzu, Inji Koci Guardiola..

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng