Rio Olympics: Najeriya zata buga wasa da Germany ba da dan wasa Azubuike ba

Rio Olympics: Najeriya zata buga wasa da Germany ba da dan wasa Azubuike ba

Dan wasan gaban Najeriya Etebo wanda kuma ke zaman wanda yafi kowa zura kwallo ka iya buga wasan da kasar sa zata buga da kasar Germany a wasan kusa da na karshe da za'ayi gobe laraba 17 ga watan Agusta inji mai magana da yawon yan wasan Timi Ebikagboro.

Wannan dai ya biyo bayan wasu rahotanni dake yawo na cewar wai an maido wasu yan wasa biyu gida Najeriya saboda rashin kudi. Yan wasan da akace an maido sune Stanley Dimgba da mai tsaron gida Yusuf Mohammed.

Sai dai mai magana da yawun yan wasan yace ba koro su akayi ba don ganin damar su ne suka dawo gida. A wani labarin kuma dan wasa Azubuike Okechukwu ma ba zai buga wasan da za ayi ba gobe saboda katin da ya samu a wasan da ya gabata.

Mai karatu dai zai iya tunawa cewar Etebo ya zura kwallaye 4 a wasan da kasar Najeriya ta buga na farko da kasar Japan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel