Matar sarkin Kano, Sarauniya Saadatu Lamido ta cika shekaru 19 (Hoto)

Matar sarkin Kano, Sarauniya Saadatu Lamido ta cika shekaru 19 (Hoto)

Amaryan sarkin Kano kuma mace ta uku cikin matan sa, Sarauniya Saadatu Lamido ta cika shekaru 19 da haihuwa a ranar Litinin, 15 ga watan Augusta.

Matar sarkin Kano, Sarauniya Saadatu Lamido ta cika shekaru 19 (Hoto)
Sarauniya Saadatu Lamido

Yan’uwa da abokanan arziki sun taya Amaryan sarkin Kano murnar zagayowar ranar haihuwar ta, yayinda suka daura hotunan ta a shafin su na sadarwar Instagram . sarauniya Saadatu Lamido ta shirya cikin purple din kaya, dan kunne silba, kwaliyya da ya bi da kayan da kuma dankwali purple domin cika kwaliyyarta.

Ku tuna cewa, Sarauniya Saadatu yar marigayi Lamidon Adamawa ce, Muhammadu Barkindodo-Mustapha, ta auri tsohon sarkin me shekaru 55, anyi bikin ne cikin sirri a garin Yola ta jihar Adamawa a shekarar da ta shige, lokacin tana shekaru 18 da haihuwa.

KU KARANTA KUMA: Iyayen yan matan Chibok sun gaya ma Buhari da ya tattauna da yan ta’adda

A satin da ya gabata munji cewa Fani Kayode ya kai hari ga sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, kan ya zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da rashin ba goyon bayan yancin kai ga jihar Palasdinawa a lokacin da yake kan kujerar mulki.

A ranar Laraba, 10 ga watan Augusta, Sarki Muhammad Sanusi na biyu, ya bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya goyi mayan bukar yanci ga jihar Palasdinawa. Duk da haka, tsohon ministan harkokin sufurin jiragen sama,Fani Kayode, ya maida martani ga ra’ayin sarki Sanusi ta shafin san a Twitter yayi kira ga sarkin da ya rufe bakinsa, cewa kasar da ake ta da husuma a kai mallakin Isra’ilawa ne ba na Palastinawa bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng