Kungiyar Real Madrid ta dauki kofin UEFA Super Cup
– Real Madrid ta doke Kungiyar Sevilla da ci 3-2 a Kofin na UEFA Super Cup.
– Dan wasa Dani Carvajal ne yaci kwallon karshe ana saura minti daya a tashi wasa.
– Cristiano Ronaldo da Gareth Bale basu buga wannan wasa ba.
Kungiyar Real Madrid masu rike da Kofin UEFA Champions league sun kara da ta Sevilla masu UEFA Europa Cup a wasan cin Kofin UEFA Super Cup a daren jiya, inda Kungiyar ta Real Madrid tayi nasara bisa takwarar ta ta gida Spain, Sevilla da ci 3-2. Kungiyar Sevilla ce dai ta buga kwallon har ta kai gab da cin kofin kafin wasan ya kai ga Karin lokaci. Matashin dan wasa Marco Asensio ya fara leka zaren a minti na 21 da wani mugun duma, kafin Franco Vasquez yayi amfani da bahaguwar sa ya ramowa Sevilla a minti na 40. Bayan an dawo rabin lokaci kuwa, Sevilla ce dai tayi ta kwallon, har ya kai a minti na 72 ta samu finariti. Yevheniy Konoplyanka ya kuwa zuba ta a raga. A yayin da Sevilla ke tuna ta gama cin kofi, sai ga Sergio Ramos ya jefa kwallo cikin raga da kai, ana daf da shirin hura usir.
KU KARANTA: MAN UTD TA DAUKI KOFIN COMMUNITY SHIELD
Bayan an kara lokaci na minti talatin ne aka kori dan wasa Thimothee Kolodziejczak na Sevilla bayan da yayi wani sakaren duka, amma duk da haka Kungiyar ta sa ba tayi rauni ba. Yan wasan Real Madrid irin su Kareem Benzema da James Rodriguez da ma Lucas Vazquez sun barar da dama dabam-dabam na karawa. Ana cikin irin haka ne dai, a kusan mintin karshe, dan wasan bayan nan Dani Carvajal ya yanke yan wasa uku, ya zunduma wata kwallo sai cikin ragar Sevilla. Haka kuwa aka tashi Real Madrid tana mai nasara da ci 3-2. Ko a 2014 dai Real Madrid ta buge Sevilla a wasan na UEFA Super Cup.
Asali: Legit.ng