Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu

Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya yaron Asiwaju Ahmed Bola Tinubu Seyi Tinubu murnan da matarsa Layal murnan aure.

Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu

A cikin sakon da shugaba Buhari ya aika, ya baiwa ma’auratan shawara da su rike ma juna alkawari. Buhari yace “ina matukar farin cikin taya ango Oluwaseyi Afolabi Tinubu da amaryarsa Layal Jade Holm murnan aurenku a yau. Ranar aure rana ce mai muhimmanci a rayuwar duk mutum. “ina muku fatan alkhairi a da zaman tare.

“Seyi, hakkin matarka akan ka shine ka kula da matarka, kayi hakuri da ita kuma ka girmamata. “ke kuma Layal, hakkin mijinki a kanki shine girmama shi, da kuma hakuri da shi. “Seyi, mahaifinka na daya daga cikin manyan mutane a kasar nan, wanda yake kokarin sabunta Najeriya. Ya dace ka kaunace shi, kuma ka daura akan abin da ya gina. “ina taya ku murna.”

Ga cikakken wasikar:

Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu

A ranar litinin 8 ga watan agusta ne ma’auratan suka angwance a gaban kotu, inda suka samu rakiyar yan’uwa da abokan arziki. Manyan baki da suka halarci bikin sun hada da gwamnan jihar Legas Akinwunmi Ambode, mataimakiyar gwamnan jihar Legas Idiat Adebule, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma sarkin Ife Oba Ogunwusi.

Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu
Buhari ya aika sakon taya murna ga yaron Tinubu

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng